Uh Oh! You should not be able to read this. The reason is that this site uses complex stylesheets to display the information - your browser doesn't support these new standards. However, all is not lost, you can upgrade your browser absolutely free, so please UPGRADE to a standards-compliant browser. If you decide against doing so, then this and other similar sites will be lost to you. Remember...upgrading is free, and it enhances your view of the Web.

Welcome to http://www.Dandali.com: Fadi naka fadi nawa!
Menu

-o-o-

Dandali - Wasannin Tashe
Barka da zuwa Dandali.com -

Goma ta marmari, goma to wuya, goma ta daukin sallah!

Wasannin Tashe (Plays and Performances during Ramadan) are some of Hausa traditional plays and performances that usually take place during the month of Ramadan (Watan Azumi) mostly at night after braking fast (bayan an sha ruwa).
Below are descriptions of few of the many plays and performances described in Hausa;

for comments, e-mail webmaster...

Thanks for visiting and come back again as we will be adding more...

Dandali - Wasannin Tashe

Zan buga, kar ka buga


A wannan tashe akan sami yara maza kamar biyar ko shida. Yaro guda shi ake daura wa igiya a }unguru sannan a sami wani yaron ya ri}e igiyar. Daga nan sai yaro mai igiya a }unguru ya d-auki babbar sanda ya shige gaba in sun je wajen wani mai kayan sayarwa a tebur ko shago sai ya ]aga sandarsa ya ce, "Zan buga". Sai sauran 'yan tashe su ce "Kar ka buga". A wani lokaci, yaron mai igiya a ]aure yakan yi kamar zai shiga cikin shago ya bugi kayan ciki amma sai yaron da ke rike da igiyar ya jawo shi baya.

Haka za su dinga yi sai an ba su sadaka sannan su tafi. A wani lokaci }ananan yara sukan shiga gidaje a inda yaron nan kan yi }o}arin buge sandarsa a kan kwanoni ko tukwane ko da wasu kayan gida haka. A wani lokaci ma har mutumin da ke zaune yana hutawa a iya yi wa tashen. A nan sai ka ga mutumin shi kansa ne ake kamanta za a buga da sandar.Ka yi rawa

A tashen "Ka Yi Rawa" akan sami yara maza kamar guda shida zuwa takwas. Sai su za~i babban cikinsu ya yi shiga irin ta malamai. Zai sa babbar riga ta tsohuwar tabarma, karauni da doguwar takarda sannan ya sami allo da kuttun tawada ya rataya. Ga kuma gafaka da carbi da sanda. Can fuska kuma ya sami ka]ar auduga ya yi saje da hana }arya da gemu da gashin baki. Daga nan sai ya wuce gaba yaran nan na biye da shi, suna wa}a yana amsawa kamar haka:

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Ban yi ba.

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Ban yi ba.

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Ga gemun?

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Ga sajen?

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Ga gafakar?

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Ga allon?

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Ga carbin?

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Ban yi ba.

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Ina na yi?

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Malam

Wa ya gani?

Yara

Ka yi rawa kai malam ka yi rawa.

Daga nan sai malam ya ce "Bari in ta~a — bari in ta~a". Ya kuma ci gaba da tafka rawa abinsa har zuwa wani lokaci.[andu}ununu


A tashen "[andu}ununu" akan sami yara maza kamar su shida su ]aura wa ]ayansu igiya ko gyale a }ugu bayan ya tu6e daga shi sai bante ya kuma sami zargina ko ba£in tukunya ya shafe fuskarsa da shi. Daga nan sai wani cikin yaran ya kama }arshen igiyar ko gyalen ya ri}e. Idan yaran sun je wani gida ko kuma dai inda za su yi tashen sai [andu}ununu ya fara sa wa}a saura su amsa kamar haka:

[andu}ununu

Ga [andu}ununu

'Yan amshi

Sai an baka.

[andu}ununu

Gidan na uwata?

'Yan amshi

Sai an baka.

[andu}ununu

Gidan na ubana?

'Yan amshi

Sai an baka.

[andu}ununu

Gidan na ubana?

'Yan amshi

Sai an baka.

[andu}ununu

Ku bar ni in ]iba

'Yan amshi

Sai an baka.

[andu}ununu

Da ni da gidanmu?

'Yan amshi

Sai an baka.

Haka za ka ga yaran suna ta wasa, idan [andu}ununu ya yi magana sai ka ga ya zabura kamar zai tafi ya ]ebo wani abu. Amma take sai ka ga yaron nan mai igiya ya jawo shi baya yayin da sauran yara ke cewa "Sai an ba ka."Macukule

A wasan "Macukule" akan sami mutane (manyan samari) hu]u ko biyar. [ayansu yakan yi shigar Gwari. Ya sa 'yar shara ta sa}i ya kuma ]aura walki na fata. Sannan sai ya sami farar }asa ya shafa a fuskarsa. Yakan kuma rataya tsohuwar bafear tunkuya Kararna, ya kuma sami }warangwal ]in wata dabba musamman ma wajen kan ya ri}e sannan ya canza muryarsa ta yi kama da ta Gwari ya wuce yana sa wa}a saura na amsawa:

Wa}a

Salamu alaikum yau ga ba}onku na Gwari.

Amshi

Macukule

Wa}a

Shekara ta dawo

Amshi

Macukule

Wa}a

Ni ma na dawo

Amshi

Macukule

Wa}a

Zan muku tashen Gwari

Amshi

Macukule

Wa}a

Yaro ba zai iya ba

Amshi

Macukule

Wa}a

Ni ma da }yar na koya

Amshi

Macukule

Wa}a

Da Naira biyar da kaza

Amshi

Macukule

Wa}a

A can a }asarmu na Gwari

Amshi

Macukule

Wa}a

Kan kare wu da]i

Amshi

Macukule

Wa}a

Kan jaki romo, ku jin tun ba wajen idon ba

Amshi

Macukule

Wa}a

Kan }uda ku~ewa

Amshi

Macukule

Wa}a

Majina kitse ne

Amshi

Macukule

Wa}a

Kan wajaina wajaina, Kullum wadubalu wa dabge

Amshi

Macukule

Wa}a

Mhm, mhm, hm da]i

Amshi

Macukule

Wa}a

Alhaji namu yana nan

Amshi

Macukule

Wa}a

Ba Alhajin tsiya ba, Ya sha ruwa lafiya lau

Amshi

Macukule

Wa}a

Wani Alhaji na nan, Bai sha ruwa lafiya ba

Amshi

Macukule

Haka zai yi ta yi sai an ba shi sadaka sai ya canza sabon salo:

Wa}a

Allah ya saka, a ci saura da lafiya lau

Amshi

Macukule

Wa}a

Kuma za mu garinmu na Gwari

Amshi

Macukule

Wa}a

Kuma sai ba]i in mun dawo

Amshi

Macukule

Wa}a

Azizu Mannanu Allah mai yau da gobe

Amshi

MacukuleJatau mai magani


Shi ma wannan tashe manya ke yin sa. Akan sami mutane kamar biyar ko shida. [ayansu (wato "Jatau") yakan yi shiga irin ta bokaye ya sami kwando ya cika da 'yan }unshe-}unshen garin }asa, da ciyayi da tsaku-wa da dai sauransu. Sannan kuma yakan sami 'yan ga~o~in kara da sassa}e-sassa}en itatuwa iri-iri. Har ila yau kuma ya sami 'yan guntattakin fata kamar su yankin buzu da ire-irensu. Duk ya ha]a ya zuba a cikin kwandon ya ]auka a ka.

Daga nan sai ya ja gaba sauran mabiyansa ma wasu na ]auke da 'yan }unshe-}unshen "magunguna" yana sa waka suna amsawa:

Jatau

Ya Bismillah Rabbana

Amshi

Jatau

Jatau

Arahamani Rabbana

Amshi

Jatau

Jatau

Za ni bayanin magani

Amshi

Jatau

Jatau

Sai a saurara a ji

Amshi

Jatau

Jatau

Wanda duk bai san ni ba

Amshi

Jatau

Jatau

Ya zo ya gan ni ya san da ni

Amshi

Jatau

Jatau

Daji-daji na shiga

Amshi

Jatau

Jatau

Rami-rami na shiga

Amshi

Jatau

Jatau

Duk wani kogo na shiga

Amshi

Jatau

Jatau

Na hau tsauni yai ]ari

Amshi

Jatau

Jatau

Na hau bishiya tai ]ari

Amshi

Jatau

Jatau

Na shiga kogi na nutse

Amshi

Jatau

Jatau

Domin neman magani

Amshi

Jatau

Jatau

{auye-}auye na tafi

Amshi

Jatau

Jatau

Birni-birni na tafi

Amshi

Jatau

Jatau

Natafi tallar magani

Amshi

Jatau

Jatau

In ba ku bayani ]an ka]an

Amshi

Jatau

Jatau

Dawa na magani ko don yunwa ma a cire

Amshi

Jatau

Jatau

Zogala gandi mataimaki
Ana figar ka kana tsaye
Kana kallon jama'ar gari


Amshi

Jatau

Jatau

Ce]iya na magani, ko don shawara a cira

Amshi

Jatau

Jatau

Sabara na magani a tambayi mai jego aji

Amshi

Jatau

Jatau

Dashi na magani don amosanin ka a cire

Amshi

Jatau

Jatau

Bi-da-zugu na magani

Amshi

Jatau

Jatau

Sanya ma na magani

Amshi

Jatau

Jatau

Ko don maye ma a cira

Amshi

Jatau

Jatau

Ku ji yo marke na magani

Amshi

Jatau

Jatau

Ko don tari ma a cira

Amshi

Jatau

Jatau

Ciwo a cikinka ya tirni}e

Amshi

Jatau

Jatau

Ka sami ma]aci magani

Amshi

Jatau

Jatau

Butar duma ma na magani

Amshi

Jatau

Jatau

Ko don alwalla a cira

Amshi

Jatau

Jatau

Kun ji rake na magani
In an yi mazar}waila ku sha


Amshi

Jatau

Jatau

Kukkuki na magani saboda jima ma a cira

Amshi

Jatau

Jatau

Wake na magani ko don yunwa ma cire

Amshi

Jatau

Jatau

Kaba na magani ko don tabarma a cira

Amshi

Jatau

Jatau

Ku san gishiri na magani
Haka barkano na magani


Amshi

Jatau

Jatau

Ko a miya sai sun ha]u
ku tambayi mai tsire ku ji


Amshi

Jatau

Jatau

[orawa na magani
ko don gaskami a cira
Haka ko don kalwa a cira
Su daddawarmu mutan gari
Lalle a miya kuke gaba


Amshi

Jatau

Jatau

[ata na magani
Yalo na magani
[unya ma na magani
Kun ji kanya ma na magani
Don ko don marmari a cira


Amshi

Jatau

Jatau

Ni ne mai magani

Amshi

Jatau

Jatau

Na gama zancen magani
Daga nan ni kam gaba zan nufa


Amshi

Jatau

Jatau

Sai bad-i Allah ya nufa

Amshi

Jatau

Jatau

Amma ku sani ba magani
A wurin wani in ba Jallah ba


Amshi

Jatau

Jatau

Allah ne mai magani
Ko gunsa ka dage ya isa


Amshi

JatauSource:
WASANNIN TASHE
Muhammad Balarabe Umar
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami'ar Bayero, Kano


^
^
Top

<---The End--->

Thats all folks!

::Home::

^
^
Top

©2001 by Dandali.com

]{}~_|[
k-}
d-]
D-[
b-~
N-_
B-|
K-{

Sub MenuLinks